Isa ga babban shafi
Wasanni

Zidane ya jagoranci ‘yan wasa da nasara

Real Madrid ta yi nasara bayan doke Sporting Gijon da ci 5-1 a wasan La liga, a karo na 2 kenan da sabon kocin kungiyar Zinedine Zidane ke jansu da sa’a

Kocin Real Madrid Zinédine Zidane.
Kocin Real Madrid Zinédine Zidane. AFP PHOTO / GERARD JULIEN
Talla

Minti 18 da fara wannan wasa Madrid ta ci kwallaye 4, inda Bale ya fara ci mata wasa sai Ronaldo daya zura kwallaye 2, da kuma Benzema, daya kara mata ta 5 minti 4 aje hutu rabin lokaci

Ita kuwa Sporting Gijon ta zura kwallon ta guda ne ta hannu Isma Lopez, bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma a wannan fafatawar Bale da Benzema sun ji rauni, abin daya kai ga canza ‘yan wasan da Jese da Kovacic.

Hukumar FIFA dai ta dakatar da Real Madrid da Atletico Madrid daga sayo ‘yan wasa na tsawon shekaru 2, saboda karya wasu dokokin kasuwar musayar yan wasanni da kungiyoyin sukayi.

Kazalika a Wasansu Valencia da Rayo Vallecano su tashi ne da ci 2-2

Gatefe ta zurawa Espanyon 3-1

Las Palmas 0-3Atl Madrid

A yanzu dai Athletico cke jan ragamar teburin na La Liga
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.