Isa ga babban shafi
La liga

Messi ne Gwarzon Spain

Lionel Messi na Barcelona aka zaba gwarzon dan wasan kwallon kafa na bana a Spain, inda ya doke abokin hamayyarsa na Real Madrid Cristiano Ronaldo.

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona Reuters/Grigory Dukor
Talla

A daren jiya ne aka yi bikin karrama ‘yan wasan na Spain a Barcelona.

Sau shida ke nan Messi na lashe kyautar a karo na bakwai da hukumar kwallon Spain ke karamma ‘yan wasan.

Messi ya ce ba karamin abu ba ne mutum ya lashe irin wannan kyauta tsakanin zaratan ‘yan wasan da ke taka kwallo a Spain.

Messi ya sadaukar da kyautar ga Dansa Thiago, dan shekaru uku, wanda ya ce kullum idan zai fita daga gida sai yaron ya tambaye shi ko zai fita ne ya ci kwallo a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.