Isa ga babban shafi
UEFA

Za a zabi gwarzon Turai tsakanin Messi da Ronaldo da Suarez

Dan wasan Barcelona Luis Suarez na Uruguay ya shiga sahun Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta ware domin zaben gwarzon dan wasanta a bana.

Lionel Messi da Luis Suárez na Barcelona da Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo
Lionel Messi da Luis Suárez na Barcelona da Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo UEFA
Talla

Dukkanin ‘Yan wasan dai na taka leda ne a gasar La liga ta Spain, kuma wannan ne karon farko da Suarez ya samu shiga sahun gwanayen kwallon a matsayin na uku bayan Cristiano Ronaldo na Real Madrid da kuma abokin wasan shi Lionel Messi.

Ana ganin dai a bana Messi ne zai lashe kyautar ta gwarzon dan wasan Turai bayan ya taka rawa a kofuna hudu da Barcelona ta lashe da suka hada da kofin gasar zakarun Turai da La liga da Copa de Ray da kuma Super Cup, sannan ya jagoranci Argentina a gasar copa America wasan karshe.

Bayan Messi da Ronaldo da Suarez, Golan Juventus ne Gianluigi Buffon aka zaba a matsayi na hudu sai Neymar na Barcelona a matsayi na biyar da Eden Hazard na Chelsea a matasayi na 6.

A ranar 27 ga watan Agusta ne za a fadi gwarzon dan wasan na Turai tsakanin Messi da Ronaldo da Suarez, inda a ranar ne kuma za a hada rukunin gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.