Isa ga babban shafi
wasanni

PSG ta kulla kwantiragin din din din da Aurier

Kungiyar nan ta kasar Faransa Paris Saint Germain ta tabbatar da cigaba da zaman Serge Aurier a kungiyar da ya kasance tare da ita a matsayin aro da Kungiyar Toulous ta bai wa PSG din

Serge Aurier
Serge Aurier Photo : PSG
Talla

Yanzu PSG ta kulla kwantiragi na din din din da Aurier, dan asalin kasar Ivory coast , kuma zai zaune a Club din har nan da watan yuni na shekarar 2019.

Aurier mai shekaru 22 ya taimakawa kasarsa ta Ivory Coast lashe kopin Afika a bana a Kasar Equitorial Guinea, kuma ya haska sau 14 a wasanni dabam dabam da PSG ta buga, sai dai kwallo daya tal ya saka a raga.
 

PSG dai bata sanar da adadin kudin da ta kashe ba na kulla kwantirgin, sai dai kafafan yada labaran Faransa na rade raden cewa kudin ya kai kimanin Euro Miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.