Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Ficewar Spain darasi ne-Alves

Dan wasan Brazil Dani Alves yace ficewar kasar Spain a gasar cin kofin duniya tun a zagayen farko babban darasi ne ga kasashen da ke fafatawa a gasar. A cewar dan wasan na Barcelona samun nasara ba karamin kalubale ba ne.

Dani Alves tare da Neymar na Brazil
Dani Alves tare da Neymar na Brazil REUTERS/Sergio Moraes
Talla

Spain ce ta lashe kofin duniya a kasar Afrika ta kudu a 2010 kuma a bana tun a tashin farko ne aka yi waje da Spain bayan ta sha kashi a hannun Holland da Chile a rukuninsu na B.

"Wannan abin kunya ne", a cewar Alves tare da yin jaje ga abokan wasan shi na Spain a Barcelona.

Wannan dai kamar kira ne Alves ya ke yi wa ‘Yan wasan Brazil don su dage musamman yadda Mexico ta rike su babu ci kafin su hadu da Kamaru a ranar Litinin domin samun hurumin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Masana dai suna ganin ficewar Brazil tun a zagayen farko babbar barazana ce ga wasannin da ta ke karbar bakunci saboda zanga-zangar adawa da wasannin da mutanen kasar ke gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.