Brazil 2014
Colombia ta doke Cote d’Ivoire
Kasar Colombia ta doke Cote d’Ivoire ci 2 da 1 a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil, Kuma ‘yan wasan Kungiyar Monaco guda biyu ne James Rodriguez da Juan Quinter suka jefa kwallayen biyu a ragar Cote I’voire a fafatawar da kasashen biyu suka yi a rukuninsu na C zagayen farko a Brazil.
Wallafawa ranar:
Talla
Gervinho ne ya samu damar zirawa Cote d’ivoire kwallo guda a ragar Colombia.
Colombia ce yanzu ke jagoracin rukuninsu na C, da maki 6, Cote d’Ivoire na matsayi na biyu da maki 3. Japan da Girka sun tashi ne babu ci a tsakaninsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu