Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Fafaroma zai yi fatawar yaki da wariyar fata

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff tace kafin a bude wasannin gasar cin kofin duniya, Wani Dan wasan Brazil zai karanta sakon fatawar Fafaroma Francis game da kyamatar wairyar launin Fata da ake nunawa bakaken ‘Yan wasa a fagen kwallon kafa.

Dan WAsan Barcelona Dani Alves yana Cin Ayabar da aka jefe shi da ita a filin wasan Kungiyar Villarreal
Dan WAsan Barcelona Dani Alves yana Cin Ayabar da aka jefe shi da ita a filin wasan Kungiyar Villarreal France 24
Talla

Shugaba Rousseff ta fadi haka ne duka kwana guda da aka jefi Dan kasar Brazil Dani Alves na Barcelona da Ayaba wanda kuma ya duka ya tsinci Ayabar ya jefa a baki yana ci a cikin filin wasan kungiyar Villarreal.

Wannan kuma ya ja hankalin shugabannin kwallon kafa a Duniya.

A shafukan dandalayen Zumunta na Facebook da twitter ‘Yan wasa da dama ne suka aika da hotunansu rike da Ayaba suna ci domin nuna goyon baya ga Alves.

Neymar na Brazil shi ne ya fara aika wa da hotonsa rike da yaba tare da sakon cewa dukkaninsu Birai ne.

Cikin ‘Yan wasan da suka bi sahu har da Luis Suarez na Liverpool da Sergio Aguero.
Wani magoyi bayan kungiyar Villarreal ne a Spain ya jefi Dani Alves da Ayaba a lokacin da kungiyar ke karawa da Barcelona.

Villarreal tace ta haramtawa magoyi bayanta day a jefi Alves da Ayaba shiga kallon wasanninta na har abada.

Amma Alves yace ya kwashe shekaru 11 a Spain kuma tun lokacin har zuwa yanzu babu wani sauyi da aka samu ga matsalar wariyar launin fata, yana mai kira ga mahukuntan kwallon kafa su dauki kwakkwaran matakai domin magance matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.