Marathon
Bekele ya lashe tseren Marathon a Paris
Dan kasar Habasha, Kenenisa Bekele ne ya lashe teren gudun Marathon da aka gudanar a birnin Paris a jiya Lahadi bayan ya yi gudun kilomita 42.195 cikin sa’oi biyu da minti 5 da dakika 4 a kewayen Paris.
Wallafawa ranar:
Talla
Abokin gudunsa na Habasha Limenih Getachew ya zo a matsayi na biyu, yayin da kuma Luka Kanda na Kenya, ya zo a matsayi na uku.
A bangaren mata ‘Yar tseren gudun kasar Kenya Flomena Cheyech ce ta lashe tseren gudun na Marathon. ‘Yar kasar Habasha Yebrgual Melese ce a matsayi na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu