Isa ga babban shafi
FIFA

Qatar 2022: Sakataren FIFA ya nemi a dage wasannin zuwa lokacin hunturu

Akwai muhawara da ta kaure a Hukumar kwallon duniya FIFA game da karbar bakuncin gasar cin kofin duniya da Qatar zata yi a 2022 inda Sakatare Janar na hukumar Jerome Valcke, yace wasannin gasar ba zasu yiyu a gudanar da su ba kamar yadda aka saba a tsakanin watan Yuni zuwa watan Yuli saboda matsanancin zafi a kasar.

Jérôme Valcke Sakate Janar na Hukumar Kwallon Duniya FIFA
Jérôme Valcke Sakate Janar na Hukumar Kwallon Duniya FIFA DR
Talla

A cewar Jerome Valcke, ya dace a dawo da wasannin a lokacin Hunturu.
Amma kuma har yanzu Hukumar FIFA ba ta amince da matakin ba, akan sai ta yi nazari tare da diba bukatar yiyuwar dage wasannin zuwa lokacin hunturu.

A shawarin Sakataren na FIFA yace ana iya gudanar da wasannin tsakanin 15 ga watan Nuwamba har zuwa watan Janairu, kamar yadda ya shaidawa Radio Faransa.

Idan dai aka dage wasannin zuwa lokacin hunturu hakan zai shafi wasannin Turai yayin da kuma Turawan ke koken ‘yan wasa zasu sha wahala idan aka gudanar da wasannin a lokacin da aka saba a kasar Qatar daboda matsanancin zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.