Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal da Djokovic za su kece raini a London

Manyan Zaratan wasan Kwallon Tennis na Duniya guda biyu Rafael Nadal da Novak Djokovic za su kece raini a wasan karshe na gasar lashe kofin Duniya na ATP da ake gudanarwa a London. 

Rafael Nadal (Hagu) Novak Djokovic (Dama)
Rafael Nadal (Hagu) Novak Djokovic (Dama) REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

A jiya lahadi Nadal ya lallasa Roger Federer ne a wasan dab dana karshe a filin Tennis na 02 Arena inda Nadal din ya ke neman kare kambunsa a matsayinsa na daya a duniya.

Djokovic kuma ya doke Wawrinka ne na Switzerland a zagayen dab da na karshe, kuma idan Djokovic ya samu sa’a akan Nadal a london zai karbe matsayin na daya a duniyar Tennis, bayan ya lashe kofin Paris Masters, idan kuma ya lashe kofin Davis Cup a Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.