Isa ga babban shafi
Qatar

An cire mutum mutumin Zidane a Qatar

Gwamnatin kasar Qatar ta cire mutum mutumin tsohon dan wasan Faransa Zinedine Zidane wanda aka kafa a birnin Doha. Hakan kuma ya faru ne saboda boren da wasu mutanen kasar suka gudanar, suna masu danganta shi da gunki wanda ya sabawa addinin Isalama.

Hoton Mutum Mutumin Zinedine Zidane Wanda ya noshi Materazzi a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a 2006
Hoton Mutum Mutumin Zinedine Zidane Wanda ya noshi Materazzi a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a 2006 ©Reuters.
Talla

A ranar uku ga watan Oktoba ne aka girka mutum mutumin na Zidane a birnin Doha wanda ke nuna nushin da dan wasan ya kai wa Materazzi na Italiya a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2006.

Amma a ranar Litinin ne aka cire mutum mutumin saboda bore da wasu suka yi. Yawanci mutanen na Qatar sun yi dogaro ne da haramcin da addinin Islama ya yi game da duk wani mutum mutumi ko zane na Dabba wanda kan iya komawa wajen bauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.