Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Mexico ta kori koci na uku cikin wata daya

Mai horar da ‘yan wasan kasar Mexico Victor Manuel Vucetich ya bayyana cewa an sallame shi a matsayin kocin ‘yan wasan kasar bayan kayi da kasar ta sha a hanun Costa Rica da ci 2-1 a wasanni fidda gwanayen da za su halarci gasar cin kofin duniya.

Tsohon mai horar da 'yan wasan Mexico, Victor Manuel Vesucith
Tsohon mai horar da 'yan wasan Mexico, Victor Manuel Vesucith laparednoticias.com
Talla

Viucetich shine mai horar da ‘yan wasa na uku da kasar ta sallama cikin wata daya.

Dan shekaru58 Vucetich ya karbi ragamar tafiyar da ‘yan wasan Mexico ne a watan Satumba da ya gabata inda ya karba a hanun Manuel de la Torre.

A lokacin ya rage mai wasannin biyu ne dai kai ‘yan wasan zuwa gasar ta Brazil inda ya fara lallasa Panama da ci 2-1 a gida.

To sai dai kayin da suka sha a hanun Costa Rica ya zo musu a bazata lamarin da ya sa burin kasar na zuwa Brazil ya fara dishewa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.