Isa ga babban shafi
Premier League

Yanzu ba da ba ne, inji Mourinho

Jose Mourinho yace ya dawo Chelsea da dubarun koyar da ‘yan wasa fiye da baya, inda yanzu ya ke neman lashe wa kungiyar Kofin Premier da kofin zakatun Turai bayan a bana ya tashi a tutar babu a Real Madrid.

Jose Mourinho na Chelsea tare da tawagar 'Yan wasan shi a Bangkok
Jose Mourinho na Chelsea tare da tawagar 'Yan wasan shi a Bangkok REUTERS/Athit Perewongmetha
Talla

Mourinho ya gargadi masoya kwallon kafa a Ingila kada su yi masa kallon sanin baya domin ya samu karin dubaru a zamansa a Inter Milan da Real Madrid.

“Farin gashi na shi ne alamun akwai sauyi” inji Mourinho a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Bangkok a ziyarar da tawagar Chelsea ta kai domin wasan zumunci.

Bayan ficewa daga Chelsea, Mourinho ya kwashe shekaru biyu a Inter Milan a Italiya kafin ya koma Spain kungiyar Real Madrid inda ya kashe shekaru uku.

Mourinho mai shekaru 50, ya lashe wa Chelsea kofin Premier karo biyu a jere da kofin gida guda biyu da kuma kofin FA a wa’adinsa na farko daga 2004 zuwa 2007.

A Inter Milan kuma Mourinho ya lashe jerin kofuna uku a shekara guda, kofin Seria A da kofin gida na Italiya da kofin Zakarun Turai. Kuma Mourinho ya lashe La liga da Copa del Ray a Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.