Isa ga babban shafi
Kasuwar 'Yan wasa

Abidal ya koma Monaco, Villa zai koma Atletico Madrid

Dan wasan Faransa na Barcelona, Eric Abidal ya kulla yarjejeniyar shekara guda da kungiyar Monaco bayan ya baro Barcelona inda ya kwashe watanni yana jinyar dashen koda da aka yi ma shi. Atletico Madrid ta cim ma yarjejeniya tsakaninta da Barcelona akan David Villa.

David Villa sanye da kayan Horo na kasar Spain a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin Duniya
David Villa sanye da kayan Horo na kasar Spain a gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin Duniya REUTERS/Andrew Innerarity
Talla

Tuni dai Monaco ta yo cefanen dan wasan Malaga Jeremy Toulalan da Ricardo Carvalho da Moutinho da James Rodriguez daga Porto da kuma Falcao na Atletico Madrid.

Monaco  tana neman gogayya ne da Paris Saint-Germain a kaka mai zuwa bayan ta hauro gasar French league karon farko tun a 2000.

Kungiyar Altletico Madrid ta cim ma yarjejeniyar cinikin dan wasan Barcelona David Villa, kamar yadda Barcelona ta sanar a shafinta na Intanet.

David Villa wanda Barcelona ta saya akan kudi Euro Miliyan 40 daga Valencia, yanzu Barcelona ta sayar da dan wasan ne akan kudi euro Miliyan 5.1, kodayake akwai sharudda a yarjejeniyar.

Kudin yarjejeniyar dan wasan euro Miliyan 5.1 ne amma Altelico Madrid zata biya kudi euro Miliyan 2.1 a wannan kakar, idan kuma dan wasan ya ci gaba da zama a kungiyar za ta sake biyan sauran kudin.

Sannan kuma kungiyar Barcelona tana da ‘Yanci kashi 50 na cinikin dan wasan a nan gaba.

Atletico Madrid  ta saye dan wasan ne domin maye gurbin Radamel Falcao wanda ya koma Monaco.

David Villa ya fara wasa ne a Sporting Gijon kafin ya koma Real Zaragoza da Valencia wanda ya zirawa kungiyar kwallaye 108.

BUNDESLIGA- SERIA A

Dan wasan Bayern Munich, Mario Gomez ya koma Fiorentina, akan kudi da aka ruwaito sun kai euro Miliyan 15 kamar yadda jaridar wasanni ta Gazzetta dello a Italia ta ruwaito

Felipe Anderson kuma na kungiyar Santos ta Brazil yanzu haka yana Rome a Italiya domin kulla yarjejeniyar shekaru 5 da Lazio.

A gobe Talata ne dai za’a diba lafiyar Dan wasan, kuma kafofin yada labaran Italiya sun ce Lazio za ta biya kudin da suka kai euro Miliyan 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.