Djokovic da Murray za su fafata a wasan karshe
Andy Murray na Birtaniya zai yi fatar kafa tarihi a matsayin baturen Ingila na farko da ya lashe kofin Tennis na Wimbledon bangaren maza tun a tsawon shekaru 77 da Fred Perry ya lashe kofin gasar a shekarar 1936.
Wallafawa ranar:
A bara Andy Murray ya sha kashi ne a hannun Roger Federer a wasan karshe, Kuma a bana dan wasan na Birtaniya zai kara ne da zakaran Tennis na duniya Novak Djokovic wanda ya ba shi kashi a gasar Asutralian Open da aka gudanar a watan Janairu.
Kodayake a bara Andy Murray ya lashe zinari a wasannin Olympics.
Wannan ne karo na Bakwai da Andy Murray ke buga wasan karshe a manyan gasa na Tennis, amma wannan ne karo na 11 da Novak Djokovic ke buga wasan karshe tare da lashe kofuna bakwai a bana.
A ranar Juma’a Djokovic ya doke dan wasan Argentina ne Juan Martin del Potro a wata karawa mafi tsawon lokaci a tarihin Wimbledon. Amma Djokovic yace haka ba zai zama cikas ba a karawar shi da Andy Murray.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu