Isa ga babban shafi
Wimbledon

Djokovic ya doke Del Potro a wasan dab da na karshe

Zakaran Tennis na duniya Novak Djokovic na Serbia ya tsallake zuwa zagayen karshe bayan ya doke dan wasan Argentina Juan Martin Del Potro a wasan zagayen dab da na karshe. A baya Djokovic ya doke Tomas Berdych na Jamhuriyyar Czeck a zagayen kwata fainal a gasar Wimbledon da ake gudanarwa a birnin London.

Dan kasar Serbia Novak Djokovic
Dan kasar Serbia Novak Djokovic Reuters/Suzanne Plunkett
Talla

Wannan ne karo na 13 da Djokovic ya tsallake zagayen dab da na karshe a manyan gasannin Tennis na duniya, Rolland Garros da Australian Open da US Open da Wimbledon

Djokovic wanda ya lashe kofin Wimbledon a 2011, a Ranar Lahadi ne zai kara da Andy Murray na Birtaniya bayan ya doke  Dan wasan Argentina Juan Martin del Potro wanda ya doke dan wasan Spaniya David Ferrer.

A shekarun baya, Djokovic ya lallasa Del Potro sau 8 amma dan wasan na Argentina ya samu sa’ar Djokovic sai uku a karawa 16 tsakanin ‘Yan wasan.

A bangaren Mata, wadanda ba’a yi hasashen za su kai labari ba su ne sun ka ba da mamaki, Kirsten Flipkens and Sabine Lisicki wacce ta yi waje da Serena Williams.

Wannan ne karon farko da Kirsten mai shekaru 27 za ta buga wasan dab da na karshe a Wimbledon bayan da ta doke Petra Kvitova, da ta lashe kofin gasar a 2011.

Kirsten za ta kara ne tsakaninta da Marion Bartoli, inda za ta yi fatar samun nasara don kafa tarihin buga wasan karshe. Bartoli sun buga wasan karshe tsakaninta da Venus Williams a 2007, amma Venus Williams ce ta lashe gasar bayan ta doke ta.

Sabine Lisicki, wannan ne karo na biyu da za ta buga wasan dab da na karshe a Wimbledon bayan ta doke Kanepi ta Estonia, ci 6-3 da 6-3.

Sai dai kuma akwai jan aiki a gabanta domin zata kara ne da ‘Yar kasar Poland Radwanska, wacce ta yi waje da Li na ta China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.