Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Barcelona ta sha kayi a hanun AC Milan da ci 2-0

Mataimakin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Jordi Roura ya bayyana cewa kayin da club dinsa ta ta sha a hanun AC Milan na da nasaba da rashin kyawun filin da aka buga wasan. Barcelonan ta sha kayi a AC Milan a jiya da ci 2-0 kuma ‘Yan asalin wasan kasar Ghana Kevin-Prince Boateng da kuma Sulley Muntari ne suka zirawa AC Milan kwallayenta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.  

Karawar da AC Milan da Barcelona su ka yi a GasarZakarun Nahiyar Turai a 2012/2013
Karawar da AC Milan da Barcelona su ka yi a GasarZakarun Nahiyar Turai a 2012/2013
Talla

A dai cewar Roura filin wasan bai cancanci a buga wasan Zakarun Nahiyar Turai a cikinsa ba, ko da yake ya bayyana cewa Barcelonan za taka rawar gani idan AC Milan ta biyo ta gida a ran 12 ga watan Maris mai zuwa.

A tarihin gasar ta Champions League AC Milan dai ta taba lashe kofin gasar sau bakwai, wato a shekarun 1963 da 1969 da 1989, da kuma shekarar 1990 har ila yau da shekarun 2003 da kuma 2007.

Real Madrid ce dai tafi kowace club yawan lashe kofin gasar inda ta samu nasarar daga kofin har sau tara, ita kuwa Barcelona sau hudu ta taba daga kofin gasar a shekarar 1992 da shekarun 2006 da 2009 da kuma 2011.

A daya bangaren kuwa, Galatasary ta kasar Turkiya da Schalke 04 sun yi kunnen doki inda suka zira kwallaye 1-1 a cigaba da gasar ta Zakarun Nahiyar Turai.

Galatasary ne dai ta fara zira kwallo a ragar Schalke 04 wacce Burak Yilmaz ya zira, kana daga baya dan wasan Schalke dan asalin Amurka Jermain Jones ya ramawa Schalke.

Hakan kuma ta faru ne duk da cewa sabbin ‘yan wasan da Galatasary da ta siyo wato, Didier Drogba da Sneijder sun bugawa club din wasa a karo na farko.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.