Isa ga babban shafi
Tennis

Azarenka da Serena sun tsallake zagaye na biyu a Australian Open

Jarumar Tennis ta Duniya Victoria Azarenka ta tsallake zagaye na biyu a gasar Australian open bayan lashe wasanta na farko. Kamar yadda Serena Williams ta sha da kyar a hannun ‘Yar kasar Romania Edina a wasan farko saboda Fama da rauni a idon kafarta. Akwai dai yiyuwar Serena da Azarenka za su iya haduwa zagayen kusa da karshe idan har sun tsallake.

Victoria Azarenka da Maria Sharapova a Sama sai a kasa Serena Williams da Li Na
Victoria Azarenka da Maria Sharapova a Sama sai a kasa Serena Williams da Li Na Reuters/Montage RFI
Talla

Tsohuwar Jarumar Tennis ta duniya ma Caroline Wozniacki ta tsallake bayan doke ‘yar kasar Jamus Sabine Lisicki.

Amma Sara Erani ta Italia ta fice gasar bayan ta sha kashi a hannun ‘Yar wasan kasar Spain Carla Suarez Navarro.

A bangaren maza kuma Andy Murray na Birtaniya ya tsallake zagaye na gaba bayan ya sha da kyar a hannun dan kasar Holland Robin Hasse.

Murray shi ne ya buga wasan karshe tsakanin shi da Novak Djokovic a bara, amma a wasan shi da Robin dan wasan ya ta yin kuskuren mika kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.