Isa ga babban shafi
Tennis

An hada ‘Yan wasan da Za su kara a Australian Open

A ranar Litinin ne za’a bude babbar gasar Australian Open, kuma a yau Juma’a aka hada ‘Yan wasa da za su kara juna. Inda Zakaran Duniya Novak Djokovic ba zai hadu da Andy Murray ba har sai a zagayen karshe.

Daga Hagu zuwa Dama: Novak Djokovic da Rafael Nadal da Roger Federer
Daga Hagu zuwa Dama: Novak Djokovic da Rafael Nadal da Roger Federer Reuters/Montage RFI
Talla

Novak Djokovic dai yana neman lashe gasar ne karo na uku kuma zai fara karawa ne da dan wasan Faransa Paul-Henri Mathieu.

Federer kuma da ke neman lashe gasar karo na biyar shi ma zai fara kece raini ne da dan wasan Faransa Benoit Paire, a yayin da kuma Andy Murray na Birtaniya zai fara karawa da dan wasan Holland Robin Haase

A bana dai za’a yi gasar ne ba tare da Rafeal Nadal ba saboda jinyar rashin lafiyar ciwon ciki da ya ke yi.

Dan Wasan Tennis na kasar Spain David Ferrer mai rike da kambun gasar Auckland ya sake tsallakewa zuwa zagayen karshe bayan doke Monfils na Faransa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.