Isa ga babban shafi
Tennis

An sauya ranar wasan karshe ta US open

Kungiyar kwararrun ‘Yan wasan Tennis ta fito ta bayyana kokenta game da sauya ranar wasan karshe da hukumar Wasan Tennis din Amurka ta yi a gasar US open daga ranar lahadi da aka saba zuwa ranar Litinin a badi.

Wasan Tennis
Wasan Tennis tennis-senegal.com
Talla

An dai saba gudanar da wasan karshe na Mata a ranar Assabar, a ranar Lahadi kuma a gudanar da wasan karshe na maza, amma hukumar wasan ta Amurka tace ta dauki matakin ne domin ba ‘yan wasa damar hutawa daga wasan kusa da karshe zuwa wasan karshe.

Sai dai kuma kungiyar kwararrun ‘Yan wasan tace matakin ya saba kai’dar sauran manyan gasanni irinsu Roland Garros da Australian Open da kuma Wimbledon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.