Isa ga babban shafi
Tennis

Serena da Venus Williams sun yi kira ga Matan Afrika su rungumi wasan Tennis

Fitattaun ‘Yan wasan Tennis na Duniya ‘yan kasar Amurka kuma ‘Yan uwan juna Serena da Venus Williams yanzu haka suna ziyara a Najeriya a karon farko domin domin yada fatawar ‘Yanci da kuma hanyoyin da za su taimaka ga ci gaban mata.

'Yan wasan Tennis Serena Williams a gefen hagu tare da Venus Williams a lokacin da suke zantawa da manema labarai a birnin Lagos na Najeirya
'Yan wasan Tennis Serena Williams a gefen hagu tare da Venus Williams a lokacin da suke zantawa da manema labarai a birnin Lagos na Najeirya Reuters
Talla

A lokacin da suke ganawa da manama labarai Serena tace sun zo ne domin taimakawa Najeriya tare da ba mata musamman yara mata kanana kwarin gwiwa don sanar da su cewa suna iya cim ma duk wani guri da suka sa a gaba a rayuwa.

‘Yan wasan sun musanta zargin su ‘Yan asalin Najeriya ne kamar yadda ake yayatawa tsakanin ‘Yan Najeriya, ‘Yan wasan sun ce suna son Afrika amma su Amurkawa ne.

A yau Alhamis ne dai ‘Yan wasan za su kai ziyara makarantun mata, a gobe Juma’a kuma su kara da juna a birnin Lagos kafin su mika zuwa kasar Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.