Isa ga babban shafi
Bundesliga

Gasar Bundesliga ta cika shekaru 50 a Jamus

A kakar wasan bana ne Gasar Bundesliga ta kasar Jamus ke bukin cika shekaru 50 da farawa, inda a yau Juma’a, Borussia Dortmund mai rike da kofin gasar za ta fara karawa da Werder Bremen a filin wasa na Iduna Perk, ana hasashen ‘Yan kallo sama da 80,000 za su kalli wasan.

Kungiyar Bayern Munich a  Bundesliga.
Kungiyar Bayern Munich a Bundesliga. Reuters
Talla

An fara Bundesliga a shekarar 1963. Kuma gasar ita ce ta biyu da samun habakar tattalin arziki bayan gasar Premier ta ingila.

Sai dai kuma tsadadden dan wasa a Bundesliga shi ne Mario Gomez da Bayern Munich ta saya hannun Stuttgart akan kudi euro miliyan 35 a shekarar 2009 idan aka kwatanta da Critiano Ronaldo da Real Madrid ta saya euro miliyan 94 a shekarar hannun Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.