Brazil
Majalisar Brazil ta amince a sayar da Giya a filin wasa
Majalisar Dattijai a kasar Brazil ta amince a sayar da giya a lokacin gudanar da gasar cin kofin Duniya, kamar yadda hukumar FIFA ta bukata duk da ’Yan adawa sun kalubalanci kudirin cikinsu har da Tsohon dan wasan kasar Romario.
Wallafawa ranar:
Talla
Yanzu kudirin ya shiga mataki na karshe inda ake neman amincewar shugabar kasa Dilma Rousseff kafin halatta sayar da giya a filayen wasa.
Tun a shekarar 2003 ne aka haramta shan Giya a filiyen wasa, kuma wasu ‘Yan majalisa sun ce sake halatta shan Giyar zai iya haifar da rikici musamman adawa tsakanin Brazil da Argentina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu