Boxing
Klitschko ya yi suka ga gwamnatin Ukrain
Zakaran Damben Boxin na duniya Vitali Klitschko ya yi kiran kaddamar da bincike bayan zargin gwamnati da fatali da kudaden shirya gasar cin kofin Turai da za’a gudanar a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Vitali Klitschko wanda shugaban wata jam’iyyar adawa ce a kasar, yace al’ummar kasar Ukrain suna neman a yi masu bayanin kudaden da gwamnati ta kashe wajen gina filin wasa inda ya yi zargin an kara kudi kusan kashi 50.
Sau biyu dai Vitali Klitschko yana shan kaye a zaben da aka gudanar a 2006 da 2008 domin neman kujerar mahajin garin birnin Kiev.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu