Isa ga babban shafi
Boxing

Muhammad Ali zai yi bukin cika shekaru 70

Muhammad Ali Tsohon Zakaran Dambem Boxing na duniya ajin masu nauyi zai yi bukin cika shekaru 70 na haihuwa. Shekaru 30 dai da suka gabata ana danganta rayuwar Ali matsayin mutum mai kokarin kyautatawa al’umma musamman wata cibiyarsa da ya bude a mahaifarsa birnin Louisville da ake tunanin har ya mutu za’a ci gaba da tunawa da shi.

Karawar Muhammad Ali da Joe Frazier a Birnin New York
Karawar Muhammad Ali da Joe Frazier a Birnin New York © Getty Images / B. Bennett
Talla

Duk da wata cuta da Muhammad Ali ke fama da ita a jikinsa, an bayyana cewa cibiyarsa na taimakawa da abinci da magani ga kananan kasashe mabukata musamman Afrika.

Muhammad Ali dai yana cikin ‘yan damben Boxing da tarihin boxin a Duniya ba zai taba mantawa da su ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.