Isa ga babban shafi
Boxing

Vitali Klitschko zai kara da Chisora na Birtaniya

Zakaran Damben Boxing ajin masu nauyi Vitali Klitschko dan kasar Ukrain ya sanar da cewa a ranar 18 ga watan Fabrairun badi ne zai yi fada da Dereck Chirosa na birtaniya a Munich. Da dadewa ne Chisora ke neman fada da Vitali amma Dan amben ke ficewa saboda fama da rauni.

Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing  tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek
Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek REUTERS/Peter Andrews
Talla

Sai dai yanzu haka Klitschko yace a shirye yake, kuma babu abinda zai dauki hankalinsa. Kodayake yace zai yi Ritaya nan bada jimawa ba.

A watan Yuli Tyson Fury ya doke Chisora a wasannin Commonwealth amma Dan damben yace zai nunawa Klitschko cewa zamaninsa ya kawo karshe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.