Isa ga babban shafi
Wassani

Wassanni Kokowar galgajiya ta kasashen ECOWAS

Kasar Senegal, ta yi nassarar samun koffin kasashen Afrika ta Yamma a wanan shekara a bangaren kokowar galgajiya inda ta lashe kasar tarrayar Najeriya da ci 4 da 1.Kasar ta senegal ta hida kasar Nijara karo na kusa da na karshe da ci 3 da 2.Kasar ta Senegal ta samu gallar zinariya 3 da ta gangar-ruwa guda.Kasar Tcheque ta yi murabus daga magana shiga takarar wanda zai doki nauyin shirya wassar Olympique ta 2020 sabi da matsalolin masu gudan rana da kasar ta hango.Magajin garin Prague babban birnin da zai doki nauyin gudanar da wassanin shi ne ya furuta hakan. A kasar Afrika ta kudu,tun ranar 25 ga watan Mayu kasar ta yi watsi da maganar dokar nauyin gudanar da wassannin Olympique na shekarata ta 2020 , domin tara kudin tallafama talawan kasar,to sai ga shi kamar cikin mafalki a yau ministan ma’aikatar lamuren motsa jiki na kasar Fikile Mbalula ya furuta cewa kasar na neman gurbin gudanar da wassanin Olympique na shekara ta 2020.Wajen milyin 50 na daalar Amurika ne za a kashewa wajen neman wana gurbi. Hukumar wassar Criket ta kasar Sri Lanka na neman gwamnatin kasar da ta bata million 69 na dallar Amurika dangance da wassar cin koffin wassar ta duniya da ta gudana a shekara bana 2011.A kasar ta Sri Lanka bayan wani bincike yan wassar Kwallon zari-ruga na kasar guda 3, sunamunce da cewa sun yi anfani da muyagun kwayoyi masu kara kuzari a lokacin kwamballar kasashe 5 na Asiya.Babban jami’in assibitin binciken irin wanan lamari shi ne ya furuta hakan a yau.  

Yan kokowar galgajiya na kasashen Afrika ta Yamma a kasar Senegal
Yan kokowar galgajiya na kasashen Afrika ta Yamma a kasar Senegal
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.