Isa ga babban shafi

An sake bude katafariyar hasumiyar Eiffel Tower bayan yajin aikin ma'aikata

An sake bude hasumiyar nan ta Paris wato Eiffel Tower bayan ma’aikatan wurin yawon bude idon sun janye yajin aikin da suka shiga na tsawon kwanki 6 a jere.

Masu yawon bude ido a hasumiyar Eiffel Tower da ke birnin Paris na kasar Faransa.
Masu yawon bude ido a hasumiyar Eiffel Tower da ke birnin Paris na kasar Faransa. REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Ma’aikan sun tsunduma yajin aikin ne domin neman sauyi a tsarin yadda ake gudanar da wurin  shakatawar tare da neman a kara kudaden da ake kashewa domin kula da hasumiyar.

A yanzu haka dai an cimma matsaya tsakanin hukumar gudanar da wurin yawon shakatawar da ma’aikatan, har ma an bude mashigar hasumiyar ga masu yawon bude ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.