Isa ga babban shafi

Faransa ta rage hasashen ma'aunin tattalin arzikinta na wannan shekarar

Ministan Kudin Faransa Bruno Le Maire ya ce gwamnatin kasar ta rage hasashenta na karuwar ma’aunin karfin tattalin arzikinta na shekarar 2024 zuwa kashi 1 cikin 100 maimakon kashi 1 da digo 4 a sakamakon yakin Ukraine da yakin Gaza da kuma koma bayan da aka samu na cinikayya tsakaninta da manyan abokan cinikayyarta Jamus da China.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da ministan kudi da tattalin arzikin kasar Bruno Le Maire.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da ministan kudi da tattalin arzikin kasar Bruno Le Maire. via REUTERS - POOL
Talla

Bruno Le Maire ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan Talabijin na Faransa TF1, inda ya ce za a rage kudaden da ake kashewa a dukkan hukumomin gwamnatin kasar da Yuro biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 10 da miliyan 800.

Ministan ya kara da cewa ba za a kara kudin haraji ba kuma ba za a rage kudaden da ake biyan ‘yan kasar ba, amma ya jaddada cewa dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su rage adadin kudaden da suke kashewa.

A cewarsa za a rage Euro biliyan biyar na kudaden gudanar da ayyuka ga dukkan ma'aikatu da kuma wasu biliyan biyar na aiwatar da manufofin jama'a, da biliyan daya na taimakawa jama'a, da kuma karin Euro biliyan daya na tallafin gyaran gidaje.

Kazalika ya ce za a kara rage wata biliyan guda daga kasafin kudin ma'aikatun jihohi da suka hadar da hukumar kasuwanci ta Faransa.

Ministan ya kuma ce gwamnatin Faransa za ta ci gaba da kokarin ganin ta cimma burinta na rage gibin da kasar ta samu a ma’aunin karfin tattalin arzikinta na wannan shekarar zuwa kashi 4 da digo 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.