Isa ga babban shafi

Zelensky ya ce dakarun Ukraine sun dakile harin da Rasha ta kai kudancin kasar

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky   y ace dakarun kasarsa sun dakile wani harin da Rasha ta kaai garin Avdiivka da ke gabashin kasar, kuma sun yi  tsayuwa irin ta daka sakamakon da zazzafar ba-ta-kashi ya biyo baya.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky. AFP - YVES HERMAN
Talla

Zelensky da  wasu manyan kwamandodji  sojinsa sun ziyarci Kherson na kudancin kasar, inda suka tattauna halin da ake ciki a garuruwan Avdiivka da Kupiansk, inda dakarun Rasha suka zafafa hare-hare.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Telegram, Zelensky ya jinjina wa dakarun da suka ja daga a wadannan yankuna, inda ya bukace su su ci gaba da tarwatsa wadanda ya bayyana a mastayin  ‘masu mamaya’.

Ofishin shugaban kasar na Ukraine ya ce an tafka asarar rayuka da ana kayan yaki a harin da Rashar ta kai Avdiivka, sai dai bai yi Karin bayani a game da hakan ba.

Rasha ta yi bayanin cewa ita ta yi nasara a wannan gwabzawa da aka yi  a Avdiivka,  kamar yadda Ukraine  ta yi tun da farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.