Isa ga babban shafi

Rasha ta kakkabo jiragen yakin Ukraine marasa matuka 19 a yankin Crimea

Rasha ta sanar da cewa ta lalata jiragen Ukraine marasa matuka guda 19 a yankin Crimea da Moscow ta mamaye da kuma tekun Black Sea.

Wani hoto da ken una yadda manyan motoci ke konewa, biyo bayan hare-haren da jiragen yakin Rasha marasa matuka suka kai a yankin Odesa, a lokacin da sojojin Rasha suka mamaye Ukraine, ranar 13 ga Satumba, 2023.
Wani hoto da ken una yadda manyan motoci ke konewa, biyo bayan hare-haren da jiragen yakin Rasha marasa matuka suka kai a yankin Odesa, a lokacin da sojojin Rasha suka mamaye Ukraine, ranar 13 ga Satumba, 2023. AFP - HANDOUT
Talla

Ma'aikatar Tsaron Kasar ta Rasha da ta bayyana hakan a shafin Telegram ta kuma tabbatar da cewa, an dakile yunkurin wani dan kasar Ukraine na kai hari da jiragen sama marasa matuka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa an harbo wasu jirage marasa matuka uku na UV a wasu wurare daban-daban.

Kasar Ukraine ta sha kai farmaki a yankin Crimea a daidai lokacin da ita ma Rasha ke kaddamar da hare-hare, sai dai a baya-bayan nan hare-haren na kara tsananta a yayin da gwamnatin Kyiv ta sha alwashin kwato yankin tekun Black Sea, wanda Moscow ta mamaye a shekarar 2014.

A ranar 25 ga watan Agusta, Rasha ta ce ta kakkabo wasu jirage marasa matuka 42 a yankin Crimea.

Tun lokacin da Ukraine ta kaddamar da hare-hare a farkon watan Yuni, Rasha ta sha fama da hare-haren jiragen sama wadanda suka lalata gine-gine da dama ciki har da wanda aka kai birnin Moscow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.