Faransa ta karrama Malamin da wani dan ta'adda ya kashe a makaranta
Daukacin al'ummar Faransa sun karrama Malamin mai shekaru 57 Dominique Bernerd, da wani dan ta'adda ya kashe tare dajikkata wasu, lokacin wani hari da kai da wuka a wata makaranta da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Wallafawa ranar:
Harin da yayi sanadin mutuwar Malamin ya daga hankalin daukacin al’ummar Faransa, ciki har da shugaba Emmanuel Macron.
Kasar dai ta tsaurara matakan tsaro bayan da maharin ya aikata aika-aikar, a yayin da tuni gwamnati ta baza dakarun tsaro dubu 7 a sassa daban daban don tabbatar da tsaro.
Harin na Arras wani gari da ke dauke tarin Yahudawa da al’ummar Musulmi, sunyi alhini da Allah wadai da rikicin da ake gwabzawa a Gaza.
Jami’an tsaro dai sun cafke wanda ake zargi da danyen aikin mai shekaru 20 kuma dan kasar Rasha da ya halaka malamin tare da jikkata wasu uku a makarantar da yake halarta.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya bayyana cewa wadanda suka jikkatan yanzu haka sun fara murmurewa a asibiti.
Daukacin makaranrun da ke Faransa sun yi shiru na minti daya domin nuna alhini da kisan gillar da aka yiwa Malamin.
Malamin dai ya ci karo da dan ta'addan ne a yayin da ya shiga matarantar da yake aiki kuma ya daddaba masa wuka a ranar Juma'ar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu