Isa ga babban shafi

Mutane 200 ne suka mutu a hare-haren da Azerbaijan ta kai Karabakh

‘Yan awaren yankin Nagarno-Karabakh sun ce akalla mutane dari 4 ne suka, kana sama da dari 4 suka jikkata sakamakon hare-haren da Azerbaijan ta shafe tsawon yini guda tana kai wa a yankin da ke neman ballewa. 

Motocin dakarun kiyaye zaman lafiya da na Azerbaijan a yankin Nagorno-Karabakh.
Motocin dakarun kiyaye zaman lafiya da na Azerbaijan a yankin Nagorno-Karabakh. AP - Emrah Gurel
Talla

Wani mai rajin kare hakkin dan adam a yankin, Gegham Stepanyan, wanda ya tabbatar da adadin wadanda wannan matakin na Azerbaijan ya rutsa da su ya ce daga cikin mamatan, akwai fararen hula 10, cikin yara kanana 5. 

Azerbaijan ba ta yi Karin bayani a kan adadin wadanda abin ya rutsa da su a bangarenta ba, amma shugaba  Ilham Aliyev ya ce an kashe wasu dakarun  kasar, wasu kuma sun samu raunuka. 

A ranar Talata ce Azerbaijan ta aike da dakarunta dauke da manyan makaman atilari, zuwa yankin Nagarno-Karabakh, wanda ke karkashin ikon Armenia, a kokarin da take na kwatar yankin da karfi, lamarin da ya janyo barazanar sabuwar rigima tsakaninta da makwafciyarta, Armenia. 

A Larabar nan Azerbaijan ta sanar da dakatar da hare-haren da ta kaddamar a yankin Nagarno-Karabakh da ake rikici a kai, bayan da dakarun Armenia suka amince su ajiye makamai, su kuma shiga tattaunawar lalubo masalaha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.