Isa ga babban shafi

Azerbaijan ta tsagaita wuta a Karabakh bayan da 'yan aware suka ajiye makamai

A Larabar nan Azerbaijan ta sanar da dakatar da hare-haren da ta kaddamar a yankin Nagarno-Karabakh da ake rikici a kai, bayan da dakarun Armenia suka amince su ajiye makamai, su kuma shiga tattaunawar lalubo masalaha.

Wani shingen bincike na dakarun kiyaye zaman lafiyar Rasha a yankin Nagorno-Karabakh.
Wani shingen bincike na dakarun kiyaye zaman lafiyar Rasha a yankin Nagorno-Karabakh. AP - Vahram Baghdasaryan
Talla

Azerbaijan da mahukuntan Armenia sun ce dakarun kiyaye zaman lafiya na Rasha sun bijiro da yarjejeniyar dakatar da wannan rikici, kwana guda bayan da Azerbaijan ta kaddamar da abin da ta kira ‘yaki da ta’addanci’ a yankin Nagarno-Karabakh.

‘Yan awaren sun ce sun amince da batun dauke  mayakansu da kuma janyewar dakarun Armenia daga yankin a yakin da ake tsakanin Armenia da Azerbaijan tun bayan rugujewar Tarayyar Soviet.

Ma’aikatar tsaron Azerbaijan ta ce bugu da kari, za a mika dukkannin makamai a karkashin sa idon dakarun kiyaye zaman lafiya na Rasha dubu 2 da ke yankin.

Dukkannin bangarorin sun ce za a gudanar da tattaunawa

Kan batun mayar da yankin da ke neman ballewa cikin Azerbaijan a ranar Alhamis a birnin Yevlakh.Mika wuya da ‘yan awaren suka yi na a matsayin gagarumar nasara ga shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan, a kokarin da yake na maido da yankin Nagarno-Karabakh mai dimbim Armeniyawa karkashin ikon kasarsa.

Sai dai a wani abu da ke alamta cewa akwai sauran rina a kaba, shugaban Armeniya, Nikol Pashinyan, a wani jawabin da ya yi ta kafar talabijin ya ce gwamnatinsa ba ta cikin wadanda suka shata wannan yarjejeniya, yana mai cewa dakarun kasar ba sa cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.