Isa ga babban shafi

'Yan sandan Burtaniya na farautar matashin da ya tsare daga kurkuku

'Yan sandan Burtaniya na ci gaba da farautar wani tsohon sojan da aka zargi da ta’addanci bayan da ya tsere a gidan yarin da aka tsare da shi yayin da yake jiran shari’a.

Sanarwar da jami'an tsaro suka makala ba farautar matashi Daniel Khalife da ya tsare a kurkuku inda yake jiran shari'a kan zargin ta'adanci. 7/09/23.
Sanarwar da jami'an tsaro suka makala ba farautar matashi Daniel Khalife da ya tsare a kurkuku inda yake jiran shari'a kan zargin ta'adanci. 7/09/23. REUTERS - ANNA GORDON
Talla

An tsaurara bincike a wani katafaren wurin shakatawa na birnin Landan wannan Juma'a inda ake tunin ya buya a can tun tserewarsa a gidan kason.

Rundunar ‘yan sandan Biritaniya ta tabbatar da binciken da ake yi a filin shakatawa na Richmond da ke kudu maso yammacin birnin, wanda ya hada da jirage masu saukar ungulu guda biyu da jami’ai a kasa, wajen farautar Daniel Abed Khalife, matashin mai shekaru 21 wanda ya silale daga gidan yarin Wandsworth da safiyar Laraba yayin da yake aiki a bangaren girke-girke, wanda alamu ke nuna cewa ya makele ne a karkashin wata babbar motar dakon abinci da ya shiga kurkukun ya fita.

Zargin ta'addanci

Ana zargin Khalife da dasa bama-bamai na bogi a sansanin soji da kuma karya dokokin Sirrin Biritaniya ta hanyar tattara bayanan da abokan gaba za su iya amfani da su.

Rundunar sojin Burtaniya ta kore matashin daga aiki bayan kama shi a farkon wannan shekarar, amma ya musanta duk zargin da ake masa, kuma a cikin watan Nuwamba za’a yi masa shari’a.

An tsaurara matakan tsaro

Yanzu haka an tsaurar matakan tsaro a filayen tashi da saukar jiragen sama da tashar jiragen ruwa ta Dover, babbar hanyar ruwa da ke tsallakawa daga Ingila zuwa Faransa, amma an fi maida hankali kan binciken Parkmond Park, mai dazuka dake nisan kilomita 8 daga kurkukun Wandsworth.

‘Yan adawar siyasar a Burtaniya sun bukaci Karin baya ni kan yadda Khalife ya tsere daga gidan yarin da ke zama mai matsakaicin tsaro da kuma dalilin da ya sa ba a tsare shi a kurkuku mafi tsaro na kasar ba tun da farko, sai gwamnatin Conservative ta ce za a gudanar da bincike mai zaman kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.