Isa ga babban shafi
Birtaniya - ta'addanci

Harin ta'addancin ne ya kashe dan majalisar Birtaniya - 'Yan sanda

'Yan sandan Birtaniya sun ce kisan da aka yi wa dan majalisar David Amess ta hanyar daba masa wuka wani lamari ne na ta'addanci, adai-dai lokacin da 'yan majalisar dokoki ke matsa kaimi wajen tsauraran matakan tsaro bayan kisan wanda ke zama ‘yan siyasar Burtaniya na biyu dake mutuwa yayin da suke ganawa da al’ummar mazabunsu cikin shekaru biyar.

An yi wa dan Majalisar Birtaniya David Amess, da wani ya kashe da wuka addu'o'i a Mujami'ar Katolika ta Saint Peter 15/10/21.
An yi wa dan Majalisar Birtaniya David Amess, da wani ya kashe da wuka addu'o'i a Mujami'ar Katolika ta Saint Peter 15/10/21. AFP - TOLGA AKMEN
Talla

‘Dan Majalisar na Jam’iyyar Konzabatib David Amess mai shekaru 69, ya mutu sakamakon daba masa wuka a lokacin da yake halartar wani taro a mazabar sa dake kudu maso gabashin Ingila jiya Jumma’a.

'Yan sanda sun ce sun cafke wani mutum mai shekaru 25 da ake zargi, kuma suna gudanar da bincike "kan alamar alaka da tsattsauran ra'ayin Islama". kafofin watsa labaran Burtaniya da dama, sun su wanda ake zargin dan asalin Burtaniya ne wanda ke da asali daga Somaliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.