Isa ga babban shafi

Girgizar kasa mai karfin maki 5.8 ta afkawa yammacin Faransa

Wata girgizar kasa mai karfin maki 5.8, ta afkawa wasu sassa na yammacin Faransa a yammacin jiya Juma'a, inda ofishin kula da harkokin girgizar kasa na kasar ya ce ta lalata gine-gine da dama.

Girgizar kasar da ta afku a yammacin Faransa ta kai maki 5.8.
Girgizar kasar da ta afku a yammacin Faransa ta kai maki 5.8. AP - Ghaith Alsayed
Talla

Ministan kulada yanayi na kasar Christophe Bechu ya ce girgizar kasar na daya daga cikin mafi karfi da aka taba samu a yankin.

Bayanan da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya tattara sun nuna rabon da a samu girgizar kasa irin wannan a Faransa tun farkon shekarun 2000.

Cibiyar tattara bayanai da ke sa ido kan girgizar kasa ta kasar RENASS ta ce karfin girgizar kasar ya kai maki 5.3 yayin da Hukumar Kula da girgizar kasa ta Faransa BCSF ta ce karfin ta ya zarce hakan domin ya kai maki 5.8.

Bayanai sun nuna cewar gidaje da dama ne suka kasance cikin duhu bayan da girgizar kasar ta afkawa yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.