Isa ga babban shafi

Sojin Ukraine sun kwato garuruwa 3 daga hannun dakarun Rasha a kudancin kasar

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce dakarunsa sun yi nasarar kwace garuruwa 3 daga hannun Sojin Rasha a hare-haren baya-bayan da suka zafafa kansu dai dai lokacin da Moscow ke cewa Kiev ba ta samu abin da ta yi fata ba a jerin luguden wutar da ta yiwa dakarunta.

Wasu dakarun Sojin Ukraine.
Wasu dakarun Sojin Ukraine. REUTERS - JANIS LAIZANS
Talla

Bayan faro luguden wutar ba kakkautawa kan dakarun Rasha da ke rike da wasu sassa da kasar su ta mamaye a kudancin Ukraine a yammacin jiya lahadi sojin na Kiev sun kwace iko da kauyuka 3 wanda shugaba Volodymyr Zelensky ke cewa gagarumar nasara ce ga kasar sake kwato sassanta.

Sai dai sanarwar ta Ukraine na zuwa a dai dai lokacin da ma’aikatar tsaron Rasha ke cewa yunkurin sojojin na Kiev ya gaza kaiwa ga nasara a kokarin farmakar jiragen Moscow da ke kan tekun Black Sea.

Yayin zantawarsa da manema labarai, Zelensky ya bukaci ‘yan jaridun da ya ke zantawa da su cewa su sanar da Vladimir Putin nasarar da dakarun Ukraine ke yi akan sojojinsa, ya na mai cewa baza su zuba ido makwabciyar ta su ta mamaye yankunansu ba.

Wannan nasara da Ukraine ke ikirari na zuwa ne bayan karin taimakon kayakin yaki da kasashen yammacin Duniya ke ci gaba da aike mata, a bangaren guda kuma kiran wadannan kasashe ya tsananta ga Iran don ganin ta cire hannunta daga rikicin, inda shugaba Emmanuel Macron a jiya lahadi ya roki takwaransa Ebrahim Raisi kan ya daina taimakon Moscow da makamai.

Kasashen yammaci na kallon taimakon na Iran ga Rasha a matsayin wani kwarin gwiwa wajen karfafa hare-harenta a Ukraine lura da yadda jirage marasa matuka samfurin Tehran ke tasiri wajen illa ga Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.