Isa ga babban shafi

Ukraine ta kwashe dubban mutane saboda ambaliyar ruwan dam din da aka fasa

Jami’ai a Ukraine sun kwashe dubban mutane daga muhallansu a yankin gabashin kasar, bayan harin bam din da ya fasa katafaren dam na Kavokha da ke karkashin ikon Rasha, lamarin da ya haifar da ambaliyar ruwan da ta mamaye kauyuka fiye da ashirin.

Wasu mazauna garin Kherson yayin ficewa daga muhallansu, bayan ambaliyar ruwan da ta biyo bayan fasa dam din Khavoka.
Wasu mazauna garin Kherson yayin ficewa daga muhallansu, bayan ambaliyar ruwan da ta biyo bayan fasa dam din Khavoka. AP - Evgeniy Maloletka
Talla

A ranar Talata kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya yayi zama na musamman kan lamarin, bayan da kasar ta Ukraine ta bukaci hakan, sai dai har zuwa lokacin wannan rahoto babu karin bayani akan abinda kwamitin ya cimma, illa kawai gargadin da shugaban hukumar kula da ayyukan jin kai Martin Griffiths yayi kan cewar, ambaliyar da fashewar dam din ta haddasa ka iya yin muni fiye da halin da ake ciki a yanzu.

Ukraine ta ce fasa dam din da Rasha ta kwace iko da shi tun shekarar bara, wani yunkuri na sojojin kasar domin dakile shirin na kaddamar da  gagarumin farmakin kwato yankunan da dakarun mamayar suka karbe iko da su a taswon fiye da shekara guda da suka shafe suna gwabza yaki.

Ya zuwa yanzu mutane dubu 17, mahukuntan Ukraine suka ce an kwashe, daga muhallansu, bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye kauyuka 24, yayin da jami’ai suka kara da garadin cewa akwai wasu karin mutanne dubu 24 da ke cikin hatsari, muddin ba a kwashe su zuwa tudun mun tsira ba, aikin da za a aiwatar a yau Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.