Isa ga babban shafi

Baraka ta fito fili wajen nadin Sarki Charles

Yayin da a yau aka gudanar da bikin nadin Sarki Charles III a birnin London, matsalar da ke tsakanin ‘yayan gidan sarautar ta sake fitowa fili lokacin bikin, ganin yadda aka zaunar da Yarima Harry da Andrew a layi na 3 na ‘yayan gidan Sarautar, maimakon layin farko.

Yarima Harry da Matarsa Meghan.
Yarima Harry da Matarsa Meghan. POOL/AFP
Talla

Yarima Harry wanda shi ne da na biyu na sabon Sarkin, sun janye daga ayyukan da suka shafi gidan sarautar tare da uwargidansa Meghan a shekarar 2020, yayin da suka dinga cacakar mutanen gidan sarautar akan yadda suka dinga nuna musu banbanci. 

Yarima Harry da Andrew a layin na uku na wurin zaman ‘ya’yan gidan Sarautar Ingila.
Yarima Harry da Andrew a layin na uku na wurin zaman ‘ya’yan gidan Sarautar Ingila. AP - Yui Mok

 

Shi kuwa Yarima Andrew wanda kani  ne ga sabon Sarkin, ya gamu da fushin fadar ne saboda alakarsa da wani attajirin Amurka Jeffrey Epstein da kuma zargin cin zarafin mata wanda aka sasanta ba tare da zuwa kotu ba.

Mahalarta bikin sun yi wa Yarima Andrew ihu lokacin da ya isa Westminster Abbey daga fadar Buckingham tare da sauran ‘ya'yan gidan sarautar. 

 

Yarima mai jiran gado William shi ne zaune na uku a layin farko daga hagu wurin nadin sarautar mahaifinsa Sarki Charles.
Yarima mai jiran gado William shi ne zaune na uku a layin farko daga hagu wurin nadin sarautar mahaifinsa Sarki Charles. AP - Aaron Chown

 

 

Wannan ne karo na farko da Yarima Harry ya shiga cikin tawagar ‘ya'yan gidan sarautar tun bayan tonon sililin da ya musu a hirar da aka yada ta kafar talabijin. 

Uwargidansa Meghan ta ki zuwa bikin da akayi a London inda ta zauna gida a Amurka tare da ‘ya'yan ta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.