Isa ga babban shafi

Paris na shirin haramta zirga-zirga da babur mai amfani da lantarki

Al’ummar birnin Paris fadar gwamnatin Faransa na shirin kada kuri’a a gobe laraba wadda za ta fayyace yiwuwar haramta amfani da wani nau’in babur me amfani da lantarki ko akasin haka, matakin da ke zuwa sakamakon karuwar afkuwar hadurra tun bayan yawaitar babur din wanda aka gabatar shekaru 5 da suka gabata.

A gobe lahadi ake shirin kada kuri'a kan yiwuwar ci gaba da amfani da nau'in babur din ko akasin haka.
A gobe lahadi ake shirin kada kuri'a kan yiwuwar ci gaba da amfani da nau'in babur din ko akasin haka. © AFP/Thomas Coex
Talla

Faransawa dai na amfani da nau’in babur din a cikin anguwanni ko kuma a tafiya marar tazara yayinda wasu ke amfani da shi a matsayin nishadi, sai dai a baya-bayan nan ana ci gaba da samun korafe-korafe kan yadda babur din ke haddasa hadurra.

Nau’in babur din wanda ake tukashi a tsaye, galibi matasa da kananun yara suka fi amfani da shi, inda a wasu lokutan su ke gasar tsere da shi, batun da mahukuntan Paris suka bayyana a mai cike da hadari.

A shekarar 2018 ne Paris ta gabatar da nau’in babur din wanda baya gurbata muhalli a wani kokari na yaki da dumamar yanayi ta yadda kamfanoni ke bayar da aron shi ga jama’a su tuka kansu tare da dawo da shi a lokacin da suka kammala uzirinsu.

Sai dai yawaitar korafe-korafen jama’a kan yadda amfani da nau’in mashin din ke jefa rayuwar jama’a a hadari ya sanya fargabar yiwuwar dakatar da amfani da shi.

 

Kafin yanzu dai, mahukuntan birnin Paris sun sanya dokar hana amfani da nau’in mashin din a gudun da ya haura kilomita 10 cikin sa’a guda a yankuna da daman a sassan birnin.

A gobe lahadi 2 ga watan Aprilu ake shirin kada kuri’a don zaben ko dai ci gaba da amfani da mashin din ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.