Isa ga babban shafi

UEFA ta biya magoya bayan Liverpool diyya kan cin zarafinsu da aka yi a Paris

Hukumar shirya gasar gasar zakarun tarai, UEFA ta mayar wa da magoya bayan Liverpool wadanda suka halarci wasan karshe na gasar zakarun Turai da aka yi a 2022 kudin tikitinsu.

Magoya bayan Liverpool kenan, lokacin da suka yi cirko-cirko a wajen filin wasa na Stade de France da ke Saint-Denis, a Arewacin Paris, ranar 28, ga watan Mayun 2022.
Magoya bayan Liverpool kenan, lokacin da suka yi cirko-cirko a wajen filin wasa na Stade de France da ke Saint-Denis, a Arewacin Paris, ranar 28, ga watan Mayun 2022. AFP - THOMAS COEX
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wani rahoton mai zaman kansa da aka fitar wanda wanda y ace UEFA tana da alhaki kan harin da aka kai wa magoya bayan Liverpool a wasan karshe da tayi da Real Madri a birnin Paris.

Rahotanni sun ce an harbawa magoya bayan kwallon kafa barkonon tsohuwa a wajen filin wasan, bayan jinkirin da aka samu na tsawon minti 36 kafin fara wasa.

UEFA ta ce kudin tikitin da aka mayarwa ‘yan kallon ya kunshi na dukkanin magoya bayan liverpool da suka sayin tikiti sama da dubu goma sha tara.

Rahoton da aka fitar dai ya ce, duk da cewa UEFA ta bi diddigin al’amarin da ya auku ranar 28 ga watan Mayun 2022, said ai babu kwararan shaidu da za su ta kare kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.