Isa ga babban shafi

Brazil ta kama wanda ake zargi da hannu a kisan wani mai gabatar da kara na Paraguay

Rundunar ‘yan sandan  Brazil a  yau  Juma’a ta ce ta kama daya daga cikin mutanen da ake kyautata zaton suna da hannu a kisan wani mai shigar da kara na yaki da kungiyoyin da ke fataucin miyagun kwayoyi a karkashin mafia a Paraguay da Colombia a bara.

Daya daga cikin Shugabanin yan Mafia a hannun yan Sanda
Daya daga cikin Shugabanin yan Mafia a hannun yan Sanda Tony Gentile - Tony Gentile
Talla

 ‘Yan sanda sun cafke  dan kasar Paraguay mai suna Miguel Insfran mai shigar da kara na kasar Paraguay a jiya alhamis a wata unguwa da ke yammacin Rio de Janeiro na kasar ta Brazil.

Kasar Paraguay da hukumar yan sanda ta kasa da kasa Interpol sun nemi Insfran bisa safarar muggan kwayoyi, da halasta kudaden haram da sauran laifuka.

An kashe Marcelo Pecci ne a watan Mayun 2022 a gaban matarsa mai ciki yayin da suke cikin hutun amarci a tsibirin Baru na Colombia, kusa da tashar jiragen ruwa na Cartagena da ke gabar tekun Caribbean.

A bara, shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce Insfran da dan kasar Uruguay Sebastian Marset, wadanda a halin yanzu suke gudun hijira, ana zargin su da aikata wannan kisa.

Kasar Colombia ta tsare mutane bakwai bisa laifin kisan, hudu daga cikinsu, ciki har da wanda ya kai harin, sun amsa laifinsu kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru 23 a watan Yuni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.