Isa ga babban shafi

Harin bam ya kashe mutane 6 tare da jikkata 81 a Turkiya

Akalla mutane shida suka mutu yayin da sama da 81 suka jikkata a kasar Turkiya ranar Lahadi, sakamakon wata fashewa da ta auku a wata unguwa mai cinkoso dake tsakiyar Istanbul.

Anguwar Istikiat da aka samu fashewar Bam a birnin Istanbul na kasar Turkiya. 13/11/22
Anguwar Istikiat da aka samu fashewar Bam a birnin Istanbul na kasar Turkiya. 13/11/22 AP - Francisco Seco
Talla

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin na Bam da aka kai wata anguwar birnin mai dauke da rukunin kantuna, to sai dai ministan cikin gidan Turkiya Suleyman Soylu ya daura alhaki kan kungiyar Kurdawa ta PKK.

Mista Suleyman yace sun tabbatar da hakan ne bayan kama wani da ake zargi da dana bam din a anguwar mai cinkoson jama’a.

Ta'addanci

Shugaban kasar Recep Tayib Erdogan da ya yi Allah wadai da harin yace al’amari na ta’addanci.

Mataimakin shugaban kasar Turkiya Fuat Oktay da ya ziyarci anguwar Istikial da lamarin ya auku yace ana zargin wata mata da aika-aikar.

Tuni Amurka da kungiyar Tarayyar Turai da Faransa da Ukraine duk suka yi Allah wadai da harin da aka samu rasa rayuka da jikkatar mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.