Isa ga babban shafi

Macron ya sha alwashin gyara dokar fansho bayan yajin aikin kungiyoyin kwadago

Gwamnatin Faransa ta sha alwashin kawo gyara ga tsarin fansho na kasar cikin shekarar da muke da nufin magance korafe-korafen jama'a, dai dai lokacin da kungiyoyin kwadago suka faro wani yajin aiki a jiya alhamis, irinsa na farko karkashin sabuwar gwamnatin shugaba Emmanuel Macron da ke mulkar kasar a wa'adi na biyu.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. REUTERS - POOL
Talla

Yajin aikin gamayyar kungiyoyin kwadagon na CGT ya katse hada-hadar jiragen kasa wanda ya kassara zirga-zirgar jama'a ciki har da dubunnan daliban makarantu, irinsa na farko tun bayan da aka sake zaben shugaba Emmanuel Macron a watan Afrilu shekarar nan da muke ciki.

Kungiyoyin kwadago da dama ba su shiga yajin aikin ba, duk da cewa galibinsu da kuma jam’iyyun siyasa tsawon lokaci suna bayyana adawar su tare da kwashe tsawon watannin ana yi kai ruwa rana dangane da kara shekarun fansho a kasar ta Faransa.

Wannan dai ne karo na farko da jama’a suka fusata in ji wani dan majalisar mai ra'ayin rikau Alexis Corbiere daga jam'iyyar LFI, wanda ya halarci zanga-zangar dubban mutane a birnin Paris.

Macron ya kara shekarun yin ritaya daga matakin da ya kai na 62 a matsayin daya daga cikin muhimman allunan yakin neman zabensa na sake tsayawa takara, yana mai cewa tsarin da ake da shi ba shi da dorewa kuma yana da tsada sosai.

Shugaban kungiyar ta CGT Philippe Martinez ya shaidawa France 2 a ranar jiya Alhamis cewa, "Dukkan kungiyoyin kwadago a Faransa suna masu adawa da tsarin aiki zuwa shekaru 64 ko 65 domin wannan wauta ce."

Jam'iyyun siyasa masu ra'ayin rikau sun kira nasu gangamin daban a ranar 16 ga watan Oktoba domin neman karin albashi da kuma kawo karshen shirin sauye-sauyen fansho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.