Isa ga babban shafi

Mace ta farko za ta dare kujerar fira minista a tarihin Italiya

Sakamakon zaben Italiya na jiya Lahadi ya nuna cewa shugabar  jam’iyyar Brothers of Italy, Giorgia Meloni za ta kafa gwamnati nan ba da jimawa ba, karon farko kenan da jam’iyya mai tsanannin tsatsauran ra’ayi za ta ja ragamar kasar tun bayan yakin duniya na 2, kuma karon farko da mace za ta dare wannan kujera a tarihin kasar.

La dirigeante du parti de droite Frères d'Italie, Giorgia Meloni, s'adresse lors d'un rassemblement alors qu'elle entame sa campagne politique avant les élections générales du 25 septembre, à Ancône, en Italie, le mardi 23 août 2022.
La dirigeante du parti de droite Frères d'Italie, Giorgia Meloni, s'adresse lors d'un rassemblement alors qu'elle entame sa campagne politique avant les élections générales du 25 septembre, à Ancône, en Italie, le mardi 23 août 2022. © AP Photo/Domenico Stinellis
Talla

Meloni wadda ke jawabi a birnin Rome, bayan da da sakamakon da ke fitowa ya nuna cewa jam’iyyarta ta lashe kaso 26 na kuri’un da aka kada, ta ce za ta bada jagoranci ga ilahirin ‘yan kasar.

Sakamakon ya nuna cewa akalla mutum 1 cikin 4 na wadanda suka kada kuri’a a zaben na Lahadi ya kada wa jam’iyyar Brothers of Italy.

Ko da yake cikakken sakamako bai fito a hukumance ba sai zuwa yammacin Litinin din nan, manyan abokan hamayyarta sun bada kai bori ya hau, inda suka ce rana ta bace musu.

Meloni ta yi ta kasancewa  a kan gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a tun bayan da Firaminista Mario Draghi ya sanar da yin wani zabe a watan Yuli, bayan rugujewar gwamnatinsa ta hadaka.

Sakonnin taya murna dai sun fara shigowa daga abokanta a nahiyar Turai, inda Fira ministan Poland Mateusz Morawiecki da jam’iyya mai tsatsauran ra’ayi na Spain da sauransu duk suka aike da sakonni.

Italiya ta yi kaurin suna wajen yawan sauyin gwamnati, inda aka samu gwamnatoci kusan 70 a kasar tun daga shekarar 1946.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.