Isa ga babban shafi

Shugaban Italiya bai amince da murabus din Firaminista ba

Shugaban Italiya Sergio Mattarella ya ki amincewa da batun murabus da Firaministan kasar Mario Draghi ya  bijiro da shi a ranar Alhamis, a wani rikicin siyasar da kwararru suka yi kashedin cewa yana iya haddasa zaben gaggawa a kasar.

Mario Draghi, firaministan Italiya.
Mario Draghi, firaministan Italiya. © AFP
Talla

A wata sanarwa, fadar shugaban Italiya ta ce shugaba Mattarella bai hatimce murabus din Firaministan ba, kuma ya gayyace shi da ya bayyana a gaban majalisar dokokin kasar don gabatar da jawabi.

A Alhamis din nan firaministan Italiya, Mario Draghi ya bayyana aniyasar ta yin murabus, bayan da  jam’iyyar 5-Star, wadda ke cikin kawancen da ke jagorancin Italiya ta ki amincewa da kada kuri’ar nuna goyon baya gareshi, lamarin da ya jefa kasar cikin rikicin siyasa.

Wata sanarwar da ofishinsa ya fitar a safiyar Alhamis ta ce, Firaminstan zai mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasar, duba da cewa kawancen da ke goyon bayan gwamnatinsa ya gushe.

 

Yanzu shugaba Sergio Mattarella ne ya dau ragamar jagorancin kasar, kuma ya zama wajibi ya yi kokarin rinjayar Firaminitsan ya tsai da shawarar kafa wata gwamnatin rikon kwarya da za ta kai kasar ga zaben shekara mei zuwa, ko kuma ya hanzarta gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.