Isa ga babban shafi

Putin ya musanta amfani da salon katse makamashi don azabtar da Turai

Shugaba Vladimir Putin ya musanta cewa Rasha na amfani da salon katse makamashi a matsayin babban makamin azabtar da Turai, kwanaki kalilan bayan Moscow ta katse babban bututuwan gas din da kasar ke amfani da shi wajen turawa kasashen na Turai makamashi.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexey Maishev
Talla

A jawabin shugaba Putin ga taron tattalin arzikin kasashen gabashin Turai da ke gudana a birnin Vladivostok mai tashar jiragen ruwa, shugaban na Rasha ya ce shirme ne tunanin cewa kasar na katse gas da gangan.

Shugaba Putin ya diga ayar tambaya da cewa, wanne makami Rasha ke amfani da shi? yana mai cewa suna bai wa Turai dukkanin makamashin da ta ke bukata, ba tare da rage adadi ba.

A juma’ar da ta gabata ne, kamfanin gas na Rasha Gazprom ya sanar da yiwuwar bude bututun a karshen mako bayan yi masa gyara na na kwanaki 3 amma har zuwa yau laraba ba a kai ga budewa ba.

Fadar Kremlin dai ta ce takunkuman da kasashen Duniya suka sanyawa Rasha ne ya dakileta daga kammala aikin gyaran wasu bututu da za su taimaka wajen isar da makamashin.

A cewar shugaba Putin, a shirye s uke su bude duk wata hanyar isar da makamashi Turai to amma basu da zabi, domin ba Rasha ce ta sanyawa kanta takunkumin da ya hana ta fitar da makamashin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.