Isa ga babban shafi

Macron ya fara ziyara a Algeria don gyara alakar kasar da Faransa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya fara ziyarar aiki a wannan Alhamis a Algeria a wani yunkuri na dinke barakar diflomasiyya da aka samu tsakanin kasashen biyu da kuma tattauna batutuwa masu alaka da samar da makamashin iskar gas zuwa kasashen Turai.

Shugaba Emmanuel Macron.
Shugaba Emmanuel Macron. © PASCAL ROSSIGNOL/REUTERS
Talla

A bara ne dangantakar tsakanin kasashen Faransa da Algeria ta kara tsami biyo bayan kalaman da shugaba Macron ya furta, inda kasar ta nemi lallai sai ya nemi afuwa, lamarin da ya haddasa samun gagarumar matsala da kuma katse huldar diflomasiyya.

Faransa dai ta shafe shekaru 130 ta na yi wa Algeria mulkin mallaka wanda ya karkare da gagarumin rikici tsakanin bangarorin biyu sakamakon tafka yakin tsawon shekaru.

Cikin kalaman Emmanuel Macron a bara ya bayyana shakku kan wanzuwar Algeria gabanin mulkin mallakar Faransa baya ga zargin mahukuntan kasar da cusa kiyayyar Faransar a zukatan 'yan kasar.

A ziyarar ta shugaba Macron yau, da ya samu tarba daga manyan jami'an Algeria, shugaban zai tattauna batutuwa masu alaka da yadda kasar za ta yi aikin safarar makamashi zuwa Turai dai dai lokacin da katsewar makamashin daga Rasha ya jefa nahiyar a halin tsaka mai wuya.

Ka zalika ana saran ziyarar ta Macron ta zamanto mafarin daidaituwar alaka tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.