Isa ga babban shafi

An yi zanga-zanga a Spain da Morocco kan mutuwar bakin-haure

Masu zanga-zanga sun gudanar da jerin gwano a wasu biranen kasar Spain da kuma a birnin Rabat na Morocco da yammacin jiya Juma'a, don nuna rashin amincewarsu da mutuwar bakin-haure 'yan Afirka 23, yayin da jami’an tsaron kan iyaka suka murukushe su a lokacin da suka yi kokarin shiga yankin Melilla na kasar Spain daga arewacin kasar Morocco.

Masu zanga-zangar adawa da kashe bakin-haure a kasar Spain.
Masu zanga-zangar adawa da kashe bakin-haure a kasar Spain. AP - Manu Fernandez
Talla

Dubban masu zanga-zangar ne suka taru a biranen Barcelona, ​​Malaga, Vigo da San Sebastian da kuma yankin na Melilla don yin tir da manufofin dakile masu gudun hijira, da kuma tsaurara kan iyakoki.

A babban birnin kasar Morocco, wasu 'yan wakilai goma sha biyu na kungiyar hadin kan al'ummomin yankin sahara da kungiyoyin da ke taimakawa bakin-haure sun yi zanga-zanga a gaban majalisar dokokin kasar, suna masu kira ga mahukuntan kasar da su daina taka rawar 'yan sandan EU.

Tuni dai Masu gabatar da kara a Morocco suka fara yi wa wasu bakin-haure 65 shari’a, galibinsu 'yan Sudan da ake zargi da yunkurin shiga Spain daga Morocco a makon guda da ya gabata.

Akalla bakin haure 23 ne suka mutu a lokacin da kusan 2,000, akasarinsu daga yankin kudu da Sahara, suka yi kokarin kutsawa cikin Spain, a cewar hukumomin kasar Morocco, yayin da kungiyoyi masu zaman kansu suka ce akalla 37 ne suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.